A zaman Majalisar Tarayya a ranar Alhamis, ta umarci NNPCL ta soke cefanar da gidajen mai 550 na NNPC ga Kamfanin OVH.
Sannan kuma ta ce a binciki yadda aka yi harƙallar cefanar da su a asirce.
Lamarin ya taso daga wani ƙorafi da Miram Onuoha ta gabatar, wata ɗaya bayan PREMIUM TIMES ta fallasa harƙallar.
Salsalar Harƙalla Da Gidogar:
Yadda aka sayar da Gidajen Man NNPC 550 ga Oando, kamfanin man su Tinubu a asirce:
Labari ne na wata gagarimar harƙallar da a tarihin Najeriya ba a taɓa yin kamar ta a NNPC ba.
Labari ne mai tsawo kamar zaren kurkunu, wanda tilas sai dai mu taƙaita kawai.
Kowa ya sani daga yau cewa tun a ranar 1 Ga Oktoba, 2022, duk inda mai karatu ya ga Gidan Man NNPC, to rufa-rufa kawai, mallakar Oando ne, a asirce ko a fakaice.
Dalla-dalla:Wala-wala Da Gada-gadar Sayar Wa Oando Gidajen Man NNPC 550 A Asirce:
1. Da farko an yi wa ‘yan Najeriya rufa-rufar cewa Sashen Rukunin Gidajen Man NNPC ya saye Gidajen Mai 388 na Kamfanin OVH. Wato idan aka haɗa da gidajen mai 550 na NNPCL, za su zama 938 kenan.
To, ‘yan Najeriya ba su sani ba ashe gidajen mai 550 na NNPC ne aka sayar wa Kamfanin OVH.
2. Kamfanin OVH dai Oando ne ya yi kura-da-fatar-akuya. A ranar 30 Ga Yuni, 2015 Oando ya rikito ƙarin jarin Dala Miliyan 210, inda ya haɗiye kamfanin HN da na ‘Vitol’, ya sauya suna zuwa OVH.
3. Shugaban NNPCL, Mele Kyari ya naɗa tsohon jami’in OVH Energy mai suna Hubb Stocsman Shugaban Gidajen Mai na NNPC.
4. Kuma Mele Kyari ya naɗa tsohon Shugaban Gudanarwar OVH, Mumuni Dangazau, Mashawarcin Musamman na sa.
5. Daga nan sai Mele Kyari ya yi watsi da Babban Mataimakin sa, aka daina komai da shi, Kyari ya rungumi Stocksman da Dangazau.
6. Wannan ciniki dai tamkar matacce ne ya sayi rayayye, domin a lokacin, Oando ba ya samun riba a hada-hadar fetur da gas a Afrika.
7. Daga nan sai ya kasance babu ma’aikacin NNPC ko ɗaya a NNPC Retail, wato Sashen Rukunin Gidajen Man NNPC. Saboda 9 daga cikin su 12, duk daga OVH aka ɗauko su.
8. Cikin watan Yuni, 2023 sai Stocksman ya tara ma’aikatan NNPC Retail, ya ce masu za a maida Hedikwatar NNPC Retail zuwa Legas, wato inda Hedikwatar OVH ta ke kenan.
9. A ranar ce dukkan ma’aikatan su ka gane dai OVH, wato su Oando ne su ka sayi gidajen man NNPC 550, ba NNPC ne ya sayi gidajen man Oando 338 ba.
10. Dama kuma PREMIUM TIMES ta gano ashe gidajen man OVH 94 kaɗai, 100 jingina ce, sauran kuma duk na wasu ne daban.
Discussion about this post