Majalisar Tarayya ta ce a gaggauta dakatar da jami’o’i ci gaba da amsar Sabon ƙarin kuɗaɗen makaranta da wasu jami’o’i su ka fara amsa.
Ali Madaki ya gabatar da ƙorafin a ranar Talata, tare da cewa lafta wa ɗalibai kuɗaɗe za shi ba wasu damar shigar cikin gari su watsar harkokin makaranta.
Ya ce wasu har ta kai ga sun kara 200%, a kan wuraren zaman ɗalibai aka yi 100%.
Ya ce a yanzu da tsadar rayuwa ta yi wa ‘yan Najeriya zobe, ya ji tsoron cewa za su iya tayar da bore a birane da sauran garuruwa.
Ali Madaki, ɗan NNPP daga Kano, ya ce jam’ar Bayero da wasu da dama sun fara karɓa.
A lokaci ɗaya an yarda da shawarar ta sa.
Daga nan ne kuma ba tare da jinkirtawa ga, an amince da wannan kari kada ya shafi ɗaliban da ke cikin makarantu mallakar tarayya.
Discussion about this post