Shugaban Majalisar Tarayya, Tajuddeen Abbas ya ƙara yawan kwamitoci, daga 110 zuwa 134.
Kenan, Abbas ya ƙara 24 daga 110 da tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ya yi a zamanin sa.
Cikin waɗanda ya naɗa Shugabannin Kwamiti akwai waɗanda suka yi a adawa da shi a lokacin zaben Shugaban Majalisar Tarayya.
Ya naɗa tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Tarayya, Idris Wase ya zama Shugaban Kwamitin Daidaiton Ma’aikata, shi kuma Betara ya zama Shugaban Kwamitin Lura da Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja.
Shi kuma Gagdi ya sake komawa kan muƙamin sa na Shugaban Kwamitin Sojin Ruwa. Dama kuma shi ya Shugabanci Kwamitin a zamanin Femi Gbajabiamila.
An ɗauki shugabancin Kwamitin Kasafin Kuɗaɗe aka ba Abbakar daga Kano, shi kuma makusancin Shugaba Bola Tinubu, wato Faleke, ya koma Shugaban Kwamitin Kuɗaɗe.
Discussion about this post