Majalisar Dattawa ta fusata da tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari, saboda cefanar da filayen jiragen saman da Kano da Abja.
Sanata Kawu Sumaila ya gabatar da ƙorafin a zaman ranar Alhamis, da Sanata Barau Jibrin ya shugabanta.
Ya ce ba a cefanar da filayen jiragen saman Abuja da ɗaya a Kano bisa dacewa ba.
PREMIUM TIMES ta yi labarin yadda Buhari ya damƙa filin jirgin Kano da na Abuja ga Amurkawa.
Gwamnatin Tarayya ta amince a damƙa filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Kano shi da na Abuja a ƙarƙashin kulawar wani kamfanin Amurka mai suna Corporacion American Airport Consortium.
Kakakin Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Harkokin Jiragen Sama, James Odaudu a ranar Alhamis.
Haka nan kuma Majalisar Zartaswa ta amince a canja sunan Ma’aikatar Harkokin Jiragen Sama zuwa Ma’aikatar Sufurin Jirage da Kula da Sararin Samaniya nan take.
Tun dai cikin 2016 aka tsara batun damƙa hakkin kulawa da filayen jiragen saman guda biyu.
Ma’aikatar ta bayyana cewa wannan wata gagarumar nasara ce ba ƙarama ba wajen ƙoƙarin da gwamnati ke yi na inganta harkokin sufuri a faɗin ƙasar nan.
Sanarwar ta ce an bi duk wata ƙa’idar tantance darajar kadarorin da kuma duba sauran sharuddan da aka tabbatar duk ba su kauce daga bin dokokin da aka shimfiɗa bisa ƙa’ida ba.
Ya ce kamfanin na Amurka an amince da shi ne saboda shaharar sa a duniya matuƙa.
“Wannan kamfani da hedikwatar sa ke New York, ya na kula da filayen tashi da saukar jiragen sama har 53 a duniya, cikin nahiyoyi shida a duniya. A cikin 2019 ya yi ciniki na fasinjoji miliyan 82.4.” Inji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa damƙa filayen guda biyu a hannun kamfanin na Amurka zai ƙara ingancin harkokin sufuri, samar da riba mai yawa.
Sanarwar kuma dai ta ƙara da cewa an damƙa haƙƙin kula da filin jirgin Malam Aminu Kano da ke Kano har tsawon shekara 30. Shi kuma filin Nnamdi Azikwe da ke Abuja an damƙa shi har tsawon shekaru 20.
Kamfanin ya shirya tsaf zai fara biyan kuɗin na-gani-ina-so dala miliyan 7 ga filin jirgin Abuja, shi kuma na Kano za a biya dala miliyan 1.5.
An yi kintacen cewa a tsawon shekarun 30 za a samu kuɗaɗen shiga har dala biliyan 40 ko sama da haka.
“Daga cikin kuɗaɗen shiga ɗin za a tara cikin tsawon shekarun, gwamnatin tarayya za ta ɗauki kashi 70, wadda za a riƙa bai wa Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama (FAAN),
Discussion about this post