Majalisar Dattawa ta fara shirye-shiryen soke adadin shekarun ɗaukar ma’aikata a ƙasar nan.
A haka sai suka yi kira ga masu ɗaukar
ma’aikata su daina la’akari da yawan ko ƙarancin shekaru.
Sanata Abba Moro ya kawo wannan bayani, ce shata adadin shekaru a ɗaukar ma’aikata ya yi karo da Sashe 42 a Dokar Najeriya ta 1999.
Dokar ta haramta bambantawa tsakanin kowane ɗan ƙasa.
Ya ce dokar ɗaukar ma’aikata ta ƙasa da ƙasa ta ce fayyace adadin shekarun ɗaukar Ma’aikata ya na kawo asarar masu basira sosai, da asara ga tattalin arzikin ƙasa.
Moro ya taɓa yin Ministan Harkokin Cikin Gida, ya ce abin tausayi za ka ga matasa sun kammala karatun jami’a, amma su rasa samun aiki, tilas su karo karatu don su samu aikin yi.
Daga nan ya ce waɗannan ƙa’idoji ke sa matasa faɗawa cikin tafka laifukan da su ka haɗa da zamba da wasu da dama.
Discussion about this post