Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa na yankin (Arewa) Abubakar Kyari ya karbi ragamar shugabancin jam’iyyar na rikon kwarya.
Kyari ya sanar da murabus din shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu ne a ranar Litinin bayan taron uwar jam’iyyar a hedikwatar ta da ke Abuja.
Bayan haka ya sanar da cewa sakataren jam’iyyar Iyiola Omisore shi ma ya yi murabus kuma mataimakin sakataren na kasa Festus Fuanter daga jihar Filato ya maye gurbinsa.
Sai dai kuma Kyari bai bai ce komai ba game da murabus ɗin da sanata Adamu ya yi ba.
A karshe Kyari a ce bisa dalilin canji da aka samu na shugabancin jam’iyyar, an dage tarorrukan jam’iyyar da za a yi zuwa wani lokaci.
Idan ba a manta an wayi garin Litinin ne kawai da raderaden wai shugaban jam’iyyar na Kasa, Abdullahi Adamu ya yi murabus.
Duk da cewa jam’iyyar bata tabbatar da haka da wuri ba, an samu rahoton cewa Adamu ya mika wa shugaban ma’aikatan fadar gwamnati Femi Gbajabiamila wasikar yin murabus.
A baya da aka tambaye shi akai cewa yayi ba zai yi magana ba sai shugaban kasa Bola Tinubu ya dawo daga Kenya.
Jam’iyyar APC ta afka cikin ruɗani tun bayan zaɓen shugaban kasa inda wasu da dama daga cikin ƴan jam’iyyar ke ganin tafiyar shugaban jam’iyyar Adamu Abdullahi , bai yi saiti da na shugaban kasa ba, ana tafoyar ne a karkace.
Discussion about this post