Dokar Najeriya ta baiwa shugaban kasa kwanaki 60 ne bayan rantsar dashi shugaban kasa ya nada Ministocin sa. Sai dai kuma Yau kwanakin sa 56 da rantsarwa, ba a ce wa Yan Najeriya komai ba.
Ranar Juma’a ce ranar karshe da doka ta baiwa shugaban Kasa ya mika sunayen ga majalisa.
Raderadi
An bayyana cewa shugaban Tinubu ya mika sunayen ministocin tun a makon jiya, sai dai kuma majalisar ba ta iya soma tantance su ba saboda akwai canji da ake ganin za a yi a sunayen wasu da aka saka.
Misali shine, an ce a sunayen akwai sunan tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, amma kuma bayan murabus da shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu yayi, ana tunanin shine zai maye gurbin sa a matsayin shugaban jam’iyyar. A dalilin haka ya sa dole a cire sunan sa daga na ministoci.
Wani Sanata da ba ya so a fadi sunan sa ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa tabbas an kammala sunayen amma kuma wasu daga cikin jigajigan APC suka dakatar da haka. Wasu na ganin akwai wadanda ba su so a cikin sunayen da aka saka su a ciki, saboda haka suka nemi lallai a canja su.
“An riga an hada jerin sunayen, mun zauna don tattaunawa kan yadda za a tantance, amma wasu jigajigan APC su ka ki amincewa da wasu mutanen da ke cikin jerin da ya sa har yanzu shugaban kasa ke kokarin gyarawa. Shi ya sa har yanzu ba a gabatar da jerin sunayen ba.”
Dan majalisar, ya ce yana da tabbacin majalisar dattawa za ta kammala tantancewa da tabbatarwa kafin ta tafi hutu. Ko da ya bukaci tsawaita wa’adin, majalisar dattawa za ta yi hakan.”
Discussion about this post