Kotu a garin Jos jihar Filato ta yanke wa John Shedrack hukuncin zaman gidan Kaso na tsawon watanni uku bayan an kama shi da laifin sace kaji guda 100 da kudin su ya kai Naira 300,000.
Alkalin kotun Shawomi Bokkos ya yanke wannan hukunci ne bayan Shedrack ya amsa laifin da ake zarginsa da shi.
Bokkos ya bai wa Shedrack zabin biyan diyyar naira 20,000 ko zaman gidan kaso na tsawon watanni uku sannan ya biya kudin diyar naira 300,000 wa mutanen da ya sace wa kajin ko kuma ya yi zaman gidan kaso na wata shida.
Dan sandan da ya shigar da karar Monday Dabit ya bayyana cewa Ikechukwu Egwuonwu wanda aka sace wa kajin ne ya shigar da kara a ofishin ‘yan sanda dake Rantya ranar 19 ga Yuni.
“ Ikechukwu ya ce Shedrack ya shiga gidansa ba tare da izini ba ya sace masa kaji 100.
Dabit ya ce a hannun jami’an tsaro Shedrack ya tabbatar wa jami’an tsaro cewa shine ya sace kajin Ikechukwu.
Discussion about this post