Babbar Kotun Tarayya ta ce tilas Gwamnati ta fayyace yadda gwamnatin Obasanjo, ‘Yar’Adua, Jonathan da Buhari su ka kashe ‘biliyoyin dalolin Abacha’.
Kotun ta kuma ce Gwamantin Bola Tinubu ta fayyace adadin kuɗaɗen da gwamnatocin baya suka karɓo, adadin waɗanda aka sace da yarjejeniyar da aka sa wa hannu a wancan lokaci.
Babban Joji Omotosho ne ya bada umarnin a ƙarar da SERAP ta shigar: FHC/ABJ/CS/407/2020.
Omotosho ya ce: “Ya zama wajibi a cikin kwana 7 a bayyana yadda aka kashe wajen dala biliyan 5 da aka karbo da suna ‘Abacha loots”.
Daga nan kotu ta ce a gwada ayyukan da aka yi da kuɗaɗen, waɗanda suka yi ayyukan daga 1999 zuwa yanzu.”
Haka a cikin watan Satumba 2022, SERAP ta maka Buhari da Malami kotu, ta na neman su bayyana yarjejeniyar da aka yi da Amurka kan wata dala miliyan 23 da aka sace.
Ƙungiyar Bin Haƙƙin Jama’a Da Tabbatar Da Ayyuka Bisa Ƙa’ida (SERAP), ta shigar da ƙara, inda ta nemi kotu ta umarci Shugaba Muhammadu Buhari da Ministan Shari’a, Abubakar Malami su bayyana yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Gwamnatin Tarayya da Amurka.
SERAP ta nemi “a bayyana yarjejeniyar da ƙasashen biyu su ka cimma dangane da batun dawo wa Najeriya da wata dala miliyan 23 wadda marigayi Janar Sani Abacha ya sata, ya ɓoye a waje.”
A cikin watan Agusta ne aka ƙasashen biyu su ka rattaba hannu a kan yarjejeniyar Amurka za ta maido wa Najeriya dala miliyan 23 daga kuɗaɗen da Abacha ya kimshe a waje.
Dala miliyan 23 ɗin dai ƙari ne kan waɗansu dala miliyan 311.7 da Amurka ta maido wa Najeriya tun cikin 2020.
SERAP ta shigar da ƙarar mai lamba FHC/CS/1700/2022 a Babbar Kotun Tarayya, inda ta nemi kotu ta tilasta Buhari da Minista Malami su buga kwafen yarjejeniyar kowa ya gani a faɗin ƙasar nan.
Kuma SERAP ta nemi a buga dalla-dallar duk abin da ake yi da kuɗaɗen da kuma aikin da aka yi da su domin jama’a su tabbatar da cewa ba ‘sata-ta-saci-sata’ ake yi ba.”
SERAP ta bayyana wa kotu cewa Dokar Bayyana Bayanan Gwamnati a Bainar Jama’a ta bada damar a fito da bayanan kowa ya san abin da ake ciki.
“Idan aka buga yarjejeniyar, ‘yan Najeriya za su san gaskiyar lamarin abin da ake ciki, kuma hakan zai sa su riƙa sa-ido kan yadda ake kashe kuɗaɗen ana gudanar da ayyuka da su. Idan ma sacewa ake yi, duk dai za su sani.”
SERAP ta ce idan ba a sa ido ba, za a iya karkatar da kuɗaɗen ko a sake sace su.
“Domin wasu daga cikin adadin dala biliyan 5 da aka dawo wa Najeriya da su tun daga 1999, na zamanin Abacha, an sake sace kashi da dama daga cikin kuɗin.”
Lauyoyin SERAP Kolawole Oluwadare da Atinuke Adejyigbe ne su ka shigar da ƙarar.
Sun ce ‘yan Najeriya na da haƙƙin a sanar da su halin da ake ciki da kuɗaɗen da ake dawo wa Najeriya da su, waɗanda aka sata tun zamanin mulkin Abacha.
A wannan lokaci, Omotosho ya bada umarnin Gwamnati ta fayyace adadin kuɗaɗen cikin wannan makon.
Discussion about this post