A ranar Labara ce Kotu a Dei-Dei ta ba da umarnin a ci gaba da tsare Darlington Chibundu mai shekara 39 a kurkuku bayan an kama shi da laifin sace jita daya da lasifika biyu da kudin su ya kai Naira 210,000 a wani coci.
Sai dai kuma wanda ake zargi Chibundu dake zama a unguwar Koro, Dutse Alhaji a Abuja ya musanta laifin da ake zarginsa da shi.
Alkalin kotun Saminu Suleiman ya yanke hukuncin daure Chibundu a kurkukun dake Suleja har sai ranar 8 ga Agusta ranar da za a yi zama na gaba a kotun
Lauyan da ta shigar da karan Charity Nwaosu ta ce Chibundu ya saci wadannan kaya ranar 29 ga Yuni.
Charity ta ce Francis Orji wani mamban cocin ‘Assemblies of God Church’ a Dutse Makaranta ne ya kawo kara ofishin ‘yan sanda dake Dutse Alhaji ranar 29 ga Yuni.
Orji ya ce a wannan rana Chibundu ya shiga cocin da misalin karfe 8:30 na dare ya saci wadannan kaya.
Ta ce Chibundu ya saci jitan naira 70,000 da lasifikan naira 140,000.
Charity ta ce a hannun jami’an tsaro Chibundu ya amsa laifin sa kuma aka bishi har inda ya boye su aka kwaso su.
Discussion about this post