Rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ta tabbatar da cafke wata amarya mai suna Tinene Isa, bisa zargin yanke mazakutan mijinta.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Aliyu, ya tabbatar da kamen a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Laraba a Katsina.
Ya ce lamarin ya faru ne a karamar hukumar Kafur.
Aliyu, wanda bai bayyana sunan wanda aka aika ma haka ba, ya ce yana cikin mawuyacin hali inda ake kula da shi a babban asibitin Malumfashi.
Ya ce wanda ake zargin ta yi amfani da reza wajen yanke masa laifin.
“Na gaya muku, muna gudanar da bincike kan lamarin.
“ Wannan amarya ta zarce shekaru 30 bisa bayanan da muka samu, ba ta yi aure ne da wuri ba. Amma kuma ana nan ana ci gaba da bincike.
Aliyu ya ce idan aka gama bincike za a maka ta a kotu domin a hukuntata.
Discussion about this post