Shugaban kwamitin tantance ayyuka a jihar Kaduna Sabiu Sani, ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta kai ga cin kwalan wasu ‘yan kwangila da suka yi watsi da ayyukan da aka ba su bayan an biya su kuɗin aiki cif cif kuma.
Sani ya shaida haka wa manema labarai a Kaduna a lokacin da yake duba wasu ayyuka, yana mai cewa duk da an samu ci gaba da dama wajen aiwatar da kwangilolin, tabbas sai gwnati ta buɗe wa wasu ƴan kwangilan Idanu, idan ma ya kai ga sai an tasa keyar su ne sai a tasa.
” Da Yawa daga cikin kwangilolin da mu ka bi ba’asin ayyukan su ana yin su, amma wasu kuma da an biya, ƴan kwangilan sun yi watsi da aiyukan sun kama gaban su, ba su a wurin aikin.
Sani ya kara da cewa kwamitin sa ta gana da ma’aikatu da hukumomin gwamnati domin sanin kuɗaɗen da aka kashe da kuma irin ayyukan da aka yi zuwa yanzu.
” Za mu bi diddigin duka ayyukan, sannan za mu tabbatar an yi mana filla-filla, musan nawa aka kashe, na wa ya rage a biya da kuma waɗanne ne aka gama da waɗanda ba a gama ba.
” Muna so a karshen aikin mu mu mika rahoton da zai wadatar da gwamnatin Uba Sani su san inda aka fito da kuma in da suka dosa.
Discussion about this post