Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Ahmad Yerima, ya nemi Shugaba Bola Tinubu ya sasanta da ‘yan bindiga, kamar yadda tsohon shugaban ƙasa, ‘Yar’Aduwa ya yi da ‘yan ta’addar Neja-Delta.
Ya bada wannan shawara ce ga Shugaba Bola Tinubu, a ganawar da suka yi, a Fadar Shugaban Ƙasa.
Ahmed ya bayyana haka ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan ganawar sa da Bola Tinubu.
Tsohon Gwamnan wanda ya yi daga 1999 zuwa 2007, sannan ya yi sanata har zango 3, ya ce sojojin Najeriya za su iya jurewa su shafe ‘yan bindiga, to amma babbar matsalar da za ci, ba a san yawan fararen hula da za a yi asara ba, waɗanda farmaki za ya shafe su.
Tuni dai da dama na nuna rashin amincewa da shawarar da Yerima ya bayar, wasu na cewa sandan alfanu ne.
Yin sulhu a cewar sa, tsakanin Tinubu da ‘yan bindiga za ya zama alheri ga Arewa da kasa.
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Ahmad Yerima, ya nemi Shugaba Bola Tinubu ya sasanta da ‘yan bindiga, kamar yadda tsohon shugaban ƙasa, ‘Yar’Aduwa ya yi da ‘yan ta’addar Neja-Delta.
Ya bada wannan shawara ce ga Shugaba Bola Tinubu, a ganawar da suka yi, a Fadar Shugaban Ƙasa.
Ahmed ya bayyana haka ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan ganawar sa da Bola Tinubu.
Discussion about this post