Alhazan Najeriya 13 ne suka rasu a Hajjin bana.
Shugaban sashen kula da lafiyar Alhazai Isman Galadima, ya bayyana cewa Alhazai 13 ne suka rasu a lokacin aikin Hajji bana.
Duka waɗanda suka rasu sun rasu ne a lokacin tattakin zuwa hawan Arafat daga Mina da kuma dawowa, sannan kuma da lokacin jifar shaiɗan.
” Mahajjata 7 sun rasu kafin hawan Arafat, 6 kuma sun rasu a lokacin wannan tafiya. 4 a filin Arafat 3 a Mina.
Jihohin Kaduna da Osun na da mutum biyu, sai kuma sauran jihohi kamar su Legas, Filato, Yobe na da mutum ɗaya kowannen su.
Galadima ya bada shawarar kada a rika barin tsoffi da waɗanda ba su da lafiya suna zuwa Jamaraat, wurin da ake jifar Shaidan.
Bayan haka Galadima ya ƙara da cewa an samu wasu Alhazai da suka kam da Bakon Dauro mutum 3, da suna asibiti ana duba su yanzu haka.
Mutum 12 kuma sun samu shanyewar ɓangaren jiki saboda tsananin zafi, sai kuma mutum 7 da ciwon sigan su ya tashi dole aka kwantar da su a asibiti.
An samu mutum 5 da matsalar tabin hankali, sai kuma waɗanda suka yi fama da zazzaɓi mai zafin gaske.
Discussion about this post