Shugaban Hukumar Alhazai na Kasa, Hassan Zikirullah ya nuna matukar rashin jin dadin kan yadda dubban mahajjata daga Najeriya suka yi kwanakin zaman Mina a waje saboda karanci rumfuna.
Zikrullah ya shaida wa manema labarai a Makka cewa kamfanin da aka baiwa Kwangilar samar wa ‘yan Najeria wurin kwana da abinci a Mina ne ya gaza.
” Najeriya ta biya kamfanin duk kudaden da suka bukata don samar wa mahajjatan Najeriya abinci, amma suka gaza. Ba su ba mahajjatan mu abinci ba sannan kuma hatta wurin kwanciya da muka biya ba a bamu isasshe ba.
“Sama da Alhazai 52,000 suka yi kwanakin Mina, rabe a jikin rumfuna a sararin Allah-Ta’ala sannan kuma ba a ba su abinci ba, sai rarume rarume suke ta yi cikin kunci saboda gazawar mahukuntan Saudiya da kamfanonin su.
” Mai makon a ba mu rumfunan da zai dauki Alhazanmu 95,000 sai akam ba mu na mutum 43,000 ne kacal. Sannan babu abinci, kuma duk mumbiya su kudin.
” Alhazan mu sun afka cikin tsananin wahala da ba shi misaltuwa saboda gazawar mahukuntan Saudiyya da kamfanin dafa abinci da muka baiwa kwangilar ciyar da Alhazan mu.
” Sannan kuma mun ce musu lokaci ya yi su kyale mu mu rika dawainiyar samar wa Alhazan mu da abinci, saboda ko mun basu ma ba su ba mu abincin da za mu iya ci. Dole a rika yin abincin da mahajjata za su iya ci. Sannan kuma a madadin duka alhazan Najeriya, muna kira ga kamfanin dafa abinci da muka baiwa kwangila ya biya mu kudin mu tunda bai cika alkawain sa ba.
” Sannan daga yanzu za mu rika bibiyar duk wuraren da aka samar mana tun kafin lokacin aikin haji ya yi. Idan da abinda za mu kara sai mu kara, idan babu sai musan abinda za mu inganta.
Discussion about this post