Kakakin fadar shugaban kasa, Dele Alake, ya bayyana cewa gwamnatin Bila Tinubu ta taka burki, za ta sake sabon lissafi game da shirin raba wa talakawa miliyan 12 tallafin naira 8000 duk wata har tsawon watanni shida.
Idan ba a manta ba gwamnatin ta ce za ta yi haka ne domin rage raɗaɗin da talakawa fe fama da shi a dalilin cire tallafin mai da gwamnati ta yi.
Mutane da dama sun yi suka a kan wannan tsari suna masu cewa ba tsari ne da zai yi tasiri ba ganin irin tsananin matsi da ake fama da shi a kasar.
Wata mai yin sharhi akan siyasa, Hafsat Imam ta bayyana cewa raba kudi haka ba shi da wani amfani.
” Ni a nawa ganin irin wannan tsari da gwamnatin ke kokarin maimaitawa ba zai haifar da ɗa mai ido ba domin gwamnatin da ta wuce irin watandar da ta yi da maƙudan kuɗin talakawa kenan da sunan wai tallafi amma abin ya kare ne a hannun wasu ƙalilan da ba ma talakawan ba su suka fi amfana da shi.
” Idan aka yi dubi da rin biliyoyin nairorin da gwamnatin Buhari ta kashe ta hanyar irin wannan rabon da saka su aka yi a masakun Kaduna, da masana’antun dake Kano da sauran sassan kasar nan, da matasa da dama sun samu sana’a da kuma kasa da samu kudaden shigowa.
” Abinda na ke gani a matsayi na na ɗan Najeriya shine, ka da Tinubu ya faɗa cikin ruɗi irin wannan shi ma ya rika kamfatar kuɗi yana lafta wa mutane da sunan wai rage raɗaɗin cire tallafin mai. A yi nazari mai zurfi a samar da masana’antu da hanyoyin kawo sauki ga harkokin kasuwanci, sanna gwamnati ta saka hannu a harkar kiwon lafiya ta yadda ba sai talaka ya kashe makudan kudi ba kafin ya samu kiwon lafiya a asibitocin kasar nan.
A karshe Alake ya ce, akwai wasu tsaretsare da gwamnati ta bijiro da su domin talakawa da suka haɗa da raba wa manoma taki da kuma shigo da abinci domin domin a raba wa talaka wa
Discussion about this post