Gwamnatin Enugu ta kama ‘yan lPOB masu tilasta zaman gidan dole.
Sakataren Gwamnati Chidebare Onyema ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar ranar Alhamis.
An yi zaman ɗar-ɗar da tsoro a ranar Laraba, bayan mahara sun hana fita harkoki.
Wani Shugaban lPOB ya samu damar yin dokar hana fita gida.
Ekpa, ya kira cewa shi ne Shugaban Ƙasa ta Biyafara, ya ce za a yi zaman gida zuwa 10 Ga Yuli.
Sai dai kuma lPOB ɓangaren Nnamdi ta yi nisanta kanta da haka.
Gwamnatin ta ce waɗanda aka kama ba su son Jihar da alheri.
An yi ta terere da waɗanda suka aka kama ɗin a hanya.
Ba tun yanzu ba, gwqmnatin yankin kudu maso gabashin Najeriya ke fama da tsagerancin ƴan IPOB din.
Kungiyar ta saka doka a yankin gaba daya, inda saka saka dokar zaman gida dole duk ranar Litinin.
Wadanda suka karya wannan doka kashe su IPOB syke yi ko su bika har gida su wulakanta ka.
A dalilin haka ya sa mutanen yakin kudu maso gabas suka nema wa kansu zaman lafiya ta hanyar bin wannan doka, koda ko gwamnati ta ce su fito su ci gaba da al’amurorin su.
Kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra na ci gaba da yakar gwamnati da yin adawa da manufofinta yayin da ita gwamnati ke ci gaba da tsare shugaban kungiyar Nnamdi Kanu a kurkuku.
Discussion about this post