Gwamnatin jihar Adamawa ta sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 da ta saka a fadin jihar biyo bayan fasa rumbuna da ofisoshin gwamnati da aka yi a ranar Lahadin da ta gabata a babban birnin jihar, Yola.
A ranar Litinin, ‘yan sanda sun ce an kama sama da mutum 100 da ke da hannu a barkewar tashin hankali a gari Yola ranar Lahadi kuma za a gurfanar da su a gaban kotu domin ya zama darasi ga sauran batagari da ke aikata iskanci a fadin jihar.
“ Har yanzu ba a gama kamun ba,An kama wadanda ake zargi sama da 100 kuma suna hannu, Amma kuma sauran jami’an tsaro ba su kawo nasu kamun ba, za a gurfanar da su duka a gaban kotu cikin gaggawa,” in ji kakakin ‘yan sandan, Suleiman Ngoroje.
RADADIN TSADAR RAYUWA: An kafa dokar hana fita a Adamawa, yayin da talakawa su ka fara fasa kantina su na kwasar abinci
Gwamnatin Jihar Adamawa ta kafa dokar hana fita tsawon awa 24, bayan talakawa sun fara fasa rumbunan gwamnati da kantina, su na kwasar kayan abinci.
Wani ganau ba jiyau ba, ya shaida wa wakilin PREMIUM TIMES cewa wadanda su ka rika fasa shagunan sun rika yin kukan matsalar abinci ta kai su ga afkawa cikin wannan mummunar matsalar da ta kai su balle kantina.
Baya ga kayan abinci, sun rika jida har da janareto, katifu da sauran kayayyaki daban-daban daga kantinan jama’a. Haka dai wani mai suna Manu Haruna ya shaida wa wakilin mu.
Kakakin Yada Labaran Gwamnan Adamawa, Humwashi Wonosikou ne ya sanar da haka a ranar Lahadin nan da rana.
Ya ce ya zama tilas gwamnatin Adamawa ta kakaba dokar, domin ta magance yadda ‘yan iska ke kwasar ksyan jama’a.
Ya ce Gwamna Umaru Fintiri ya kafa dokar zaman gida dole, daga yau 30 ga Yuli, 2023. Kuma wannan doka ta na nufin ba fita waje tun daga yau, sai fa masu wani dalili na fita waje na musamman, kuma masu dauke da katin shaida.
Haka kuma Gwamna Fintiri ya roki a kai zuciya nesa, a daina kwasar kayan jama’a, a bi doka da oda. Ya kuma gargadi duk wanda bai ji bari ba, to zai ji hoho.
Ita ma Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa, ta gargadi jama’a cewa duk wanda ya karya doka, to ya kuka da kan sa.
Kakakin Yada Labaran su Afolabi Babatola, ya ce an baza zaratan jami’an tsaro da za su tabbatar da cewa kowa ya kiyaye umarnin zaman gida tilas da gwamnatin jihar ta kakaba.
Discussion about this post