Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewar ya na sane da matsalar tsaro da ake fama da ita a Najeriya, tare da shan alwashin zai magance matsalar gaba daya.
Ya bayyana haka a bikin Ranar Sojoji na 160, da aka yi a ranar Alhamis a Oyo.
Shettima ya halarta a madadin Bola Tinubu.
Ya sha alwashin cewa gwamnati za ta shawo kansa matsalolin harkokin tsaro, a ɗan lokaci kaɗan.
“lna daɗa jaddada alwashin cewa za a bayar da kulawa sosai ga sojoji na kasar.
“Zan myagance matsalar rashin kuɗi da ta makamai.”
Tinubu ya ce gwamnati ta ɗauko dabarun magance matsalolin da ake fama.
Ya kuma yi kira a bar abn da zai raba jama’a.
A baya-bayan nan sabon Shugaban Yan sanda ya ce, ‘Ni ne jan damisar da zai kacaccala ku’
Sabon Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya jaddada cewa a shirye ya ke ya kakkaɓe dukkan masu aikata muggan ayyuka daga ƙasar nan.
Egbetokun ya yi wannan furuci lokacin da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ke liƙa masa lambar ƙarin girma, a Fadar Shugaban Ƙasa.
Egbetokun ya gaji Usman Baba, wanda ya yi ritaya.
Ya taɓa zama Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Legas.
Ya shaida wa manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa cewa zai kama aiki a ranar Laraba.
“Jin kai na na ke yi kamar wata garjejiyar damisa, wadda ta yi shirin kacaccala maɓarnata kuma ta kori manyan masu laifi daga ƙasar nan.
“Jin kai na na ke kamar zaki mai jiran damushe maƙiya Najeriya.”
Discussion about this post