Gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya kori mai ba shi shawara na musamman kan matasa, Babangida Sarki, bisa zarginsa da yada labaran luwadi a shafin sa na Whatsapp.
Mai taimakawa gwamnan kan harkokin yada labarai, Ahmed Idris ne ya sanar da korar sa ga manema labarai a ranar Litinin.
“Gwamnan jihar Kebbi Nasiru Idris ya sauke mai ba shi shawara na musamman kan harkokin matasa Babangida Sarki.
“Korar da aka yi wa Sarki ya biyo bayan wani kazamin rubutu da ya yi ya saka a shafinsa na WhatsApp.
” Gwamnan ya fusata matuka kan waɗannan abubuwa da Sarki ya saka a shafin sa yana mai cewa jiha irin Kebbi da jihar Musulunci ace wai mutum mai muƙami irin haka yana ƴada irin waɗanan abubuwa a shafin sa.
Shi dai Sarki ya saka hotuna da rubutu na fasikanci kan luwaɗi a shafin sa na WhatsApp.
An kuma tambaye shi ko an yi masa kutse ne a shafin sa sai ya ce ba a yi masa kutse ba da sanin sa ya saka waɗannan ababe na fasikanci a shafinsa.
An nemi ji ta bakin Sarki amma wayoyin sa ba su shiga ba.
Discussion about this post