Gwamnatin Abba Yusuf ta soke karin matsayin da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta yi wa malaman Firamare da na Karamar Sakandaren jihar ,watanni biyu kafin mika mulki ga sabuwar gwamnati.
Wasu daga cikin malaman da abin ya shafa sun shaida wa PREMIUM TIMES ba su shirya wa wannan soke karin girma da aka yi musu ba, domin ya shafi albashin su.
“Gwamnatin Ganduje ta yi wa malamai Karin matsayi sau biyu inda na farko ta yi a shekarar 2017 sai na biyu a 2023 inda na samu Karin naira 14,000 a albashin da na samu na watan Afrilu da Mayu. Amma bayan da na karbi albashin watan Yuni sai na ga babu Karin naira 14,000 din da na samu. Bayan na yi tambaya ne aka sanar min cewa sabuwar gwamnati ta soke wannan tsari.
Wani malamin sakandare dake aiki a karamar hukumar Fagge ya samu Karin matsayi daga mataki 9 zuwa 13 bayan ya Yi tsawon shekaru goma yana jiran ya samu karin matsayi.
Malamin ya ce bayan ya samu Karin matsayin albashinsu ya karu daga Naira 44,000 zuwa 74,000.
“Soke Karin matsayin malamai da wannan sabuwar gwamnati ta yi ya shammaci malamai matuka.
Malaman da suka tattauna da wakilin mu sun ce a ƴan watannin nan biyu da Ganduje ya yi musu ƙarin girma sun sha jan miya. Yanzu kuwa lamari ya canja, za a koma gidan jiya.
Discussion about this post