Gwamnan Jigawa Umar Namadi ya karya farashin buhun taki a jihar Jigawa domin manoman jihar su iysa siya domin noman bana.
Gwamnan ya umarci Hukunmar ayyukan gona na jihar su siyar da kowanne buhu daya akan naira 16,000 maimakon naira 26,000 da manoma ke siya a kasuwa.
Gwamnan ya sanar da siyan tirela 200 na takin zamani domin manoman jihar.
Manoman jihar da suka zanta da wakilin PREMIUM TIMES a Jigawa sun yabawa gwamna Namadi bisa wannan hubbasa da yayi na kawo musu agajin gaggawa game da takin.
” Gaskiya badun wannan sassauci da muka samu ba, ban yi tsammanin zan iya siyan buhu ko da daya bane, domin ba ni da shi. Kowa ya san irin tsananin matsai da aka shiga a kasar nan dalilin janye Tallafin mai.” In ji Musa Isma’il
Ya kara da cewa irin haka ne mutane musamman talakawa ke bukata domin shine zai amfanar da su kai tsaye. Muna farin ciki matuka ga wannan kokari da gwamna Namadi ya yi.
Sai dai duk da wannan kokari na gwamna Namadi ya yi wasu daga cikin manoman sun shaida cewa su fa ba su da koda na siya a wannan farashin ne.
” Ni ban da kudin siya ko a naira 16,ooo da ake saida wa ma yanzu, wato farashin gwamnati. Bani da shi gaskiya.
Discussion about this post