Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya yi wa mahajjatan jihar 3,000 kyautar Riyal 300 a Makka.
Riyan 300, daidai yake da naira 75,000.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa dake dauke da sa hannun mashawarcin gwamnan kan harkokin yada labarai Mukthar Gidado da ya fitar ranar Juma’a a garin Bauchi.
Gidado ya ce gwamnan ya raba wa mahajjatan wannan kudi ne yayi da ya kai ziyara masaukin yan asalin jihar a Makka.
Ya ce ya bada wannan kyauta ne domin mahajjata su samu karin kudin guziri.
A karshe gwamnatin jihar ta ce tana taya Alhazan jihar jimamin karancin wurin kwana da aka samu a Mina, cewa gwamnati za ta duba abinda za ta iya yi domin gaba.
Discussion about this post