Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya, ta gargadi Sojojin Juyin Mulkin Nijar cewa su gaggauta sakin Shugaban Kasar, Mohammed Bazoum, wanda su ka hambarar.
Majalisar ta ce akwai bukatar a tabbatar da tsaron lafiyar sa, ran sa da na iyalan sa da mambobin gwamnatin sa duka.
Tun da farko sai da Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutteres ya fitar da wannan kakkausan gargadi ga sabbin mahukuntan sojojin Nijar, wadanda a yanzu su ke rike da mulkin kasar.
Ita ma Kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana cewa ta jingine bayar da duk wani taimako, talllafi, agaji ko gudummawar da ta ke bai wa Jamhuriyar Nijar.
Yayin da ake ci gaba da kallon-hadarin-kaji tsakanin ECOWAS da Sojojin Juyin Mulkin Jamhuriyar Nijar, ita ma Kungiyar Hadin Kan Afrika, AU, ta Kungiyar AU ta bai wa sojojin Nijar wa’adin kwana 15 su sauka, su kuma sojojin sun dunguri hancin ECOWAS.
AU ta gargardi sojojin da suka yi juyin mulkin cewa su tattara komatsan su cikin kwanaki 15 su koma barikin soja, su maida mulki a hannun farar hula.
A taron da Majalisar AU ta yi, mambobin kungiyar sun nuna matukar damuwar su dangane da juyin mulkin da aka yi a Jmahuriyar Nijar, wanda su ka ce ya kawo wa dimokradiyya koma baya, ya gurgunta tsaron kasar, kuma ya kawar da Nijar daga turbar wanzuwar kwaciyar hankali da ma Nahiyar Afrika baki daya.
AU ta kara tabbatar da cewa ba za ta taba amincvewa da mulkin soja a cikin Nahiyar ba, kuma ta nemi a gaggauta sakin shugaban da suka hambarar, Mohammed Bazoum.
Haka kuma AU ta hori sojojin Juyin Mulki su mutunta ‘yancin jama’a, lafiyar Bazoum da kuma mutuncin sa.
Mun Fi Karfin ECOWAS Ta Zare Mana Idanu – Sojojin Nijar
A ranar Asabar kuma Sojojin Juyin Mulkin Nijar su ka gargadi ECOWAS cewa ba za su yi sassaauci ga duk wani yunkurin yin amfani da karfin soja a kan sabuwar gwamnatin ta su ba.
Sun ce sun fahimci take-taken ECOWAS shi ne yin amfani da karfin soja a kan Nijar, ta hanyar hada kai da AU, har da kasashen da ba ECOWAS ba. Haka Amadou Abdramane ya bayyana.
Discussion about this post