Shugaba Bola Tinubu ya gargaɗi Shugabannin Afrika cewa ya zawa dole a girmama dimokraɗiyya da haƙƙin tsarin mulkin farar hula, matsawar dai ana so a samu ci gaban tattalin arziki da zaman lafiya.
Ya yi bayanin a Kenya, a taron da UNDP ta shirya wa Shugabannin Afrika, a ranar Asabar.
Shugaban ECOWAS ɗin ya damu da yadda soji ke yi wa farar hula shisshigi.
Ya ce tilas a kawo karshen hakan a Afrika
A lokacin da Tinubu ya zama sabon Shugaban ECOWAS, ya yi gargaɗin a daina juyin mulki a Afrika ta Yamma.
An zabi Shugaba Bola Tinubu ya zama sabon Shugaban ECOWAS, wanda a wurin ya yi gargaɗin a daina juyin mulki a Afrika ta Yamma.
Gaba ɗaya kasashen Afrika ta Yamma ne su ka yarda da cewa Bola Tinubu ya zama Shugaban ECOWAS ba tare da hamayya ba.
Haka ya faru a zaman ECOWAS na 63, da aka yi a Gini Bissau, a ranar Lahadi.
Bola Tinubu da ke sabo a cikin ECOWAS, ya yarda da wannan matsayi, a madadin Najeriya, har ma ya ce zai yi nasara sosai.
Amma kuma ya yi gargaɗin cewa matsalar tsaro a Afrika ta Yamma fa ta yi tsamari sosai. Ga kuma matsalar masu ta’addanci da yawan hamɓarar da gwamnati.
Ya ce waɗannan matsaloli na ciyar da ƙasashen yankin baya, tare da cewa dole a tashi tsaye a ceto ECOWAS daga hannun ‘yan ta’adda da masu hamɓaras da gwamnati.
Tinubu ya ce ya zama wajibi a tashi tsaye a ga cewa babu wata kasa da ke ƙarƙashin mulkin sojoji, ta hanyar tallafa wa waɗanda sojoji suke mulki a ga cewa farar hula ta zama mai mulki a ƙasashen.
Shugaban ya ce zai yi nasara wajen haɗa ƙasashe na ECOWAS a samu tattalin arziki.
A jawabin sa, Shugaban ECOWAS wanda ya bar gado, Omaro Mohtar, Embalo, ya yaba wa Shugabannin Ƙasashen Afrika ta Yamma.
Discussion about this post