Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, Taoreed Lagbaga ya gargaɗi matasan Mangu da kewaye su kawo makaman su ko sojoji su karkashe su.
Lagbaja ya yi wannan gargaɗin a taron sulhu tsakanin masu dauke da makamai su ma suna ta’addanci a Filato da kewaye.
An yi taron a cikin garin Mangu a ranar Azabar, har Kungiyar CAN, jama’tu, Miyetti Allah da ƙabilar Maugu sun halarci taron.
“Wannan gargaɗi ne ga wanda ya san yaron sa ya ɓoye bindiga, to ya gaggauta amso ta. Domin wanda aka samu da bindiga harbe shi za a yi, ba tare da biyan diyya ba.”
Faɗace-faɗace a Mangu dackewaye ya yi asarar rayuka sama da 300 daga watan Afrilu zuwa yanzu. Waɗanda suka rasa muhalli sun zarce 80,000.
A tsakiyar watan Yuli ma ya ce Sojojin Najeriya za su magance rikicin jihar Filato.
Lagbaja, ya jaddada cewa Sojojin Najeriya sun tsara hanyar magance rikicin jihar Filato.
Ya ce mafi yawan faɗace-faɗace a Filato matsala cewa tsakanin masu noma da masu kiwon a cikin wasu wurare.
Amma kuma ya ce wanda ya faru baya-bayan nan a Mangu, abin damuwa ne sosai ga sojoji da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.
“Tabbatar maka cewa wannan matsala da ka kawo inda ya fi dacewa a ɗaukar mata yadda za a iya magance ta.”
“Mun fito da wasu hanyoyi, waɗanda za a iya cewa an magance matsalar.”
Lagbaja ya ce Gwamna ya yi taro da masu ruwa da tsaki, domin a samu zaman lafiya, a bar tashe-tashen hankula.
Ya kuma shawarci Caleb da a fito da tsarin tsaro na cikin gida.
Haka kuma ya shawarci Gwamna ya fito da rahotannin baya, domin ya ga abin da ya dace a yi a baya, amma ba amma ba a yi ba.
Discussion about this post