Kotun dake sauraron kararrakin cin zarafin mata da yara kanana dake Ikeja jihar Legas ta yanke wa wani malamin makaranta mai suna Bright Emelogu dake da shekaru 27 hukuncin daurin rai da rai bayan an kama shi da laifin yi wa dan shekara 14 fyade ta dubura.
Alkalin kotun Abiola Soladoye ya ce wannan mummunar qbu da Emelogu ya aikata ya zarce gona da iri matuka.
Soladoye ya yanke wannan hukuncin bisa ga bayanin da dalibin ya gabatar da sakamakon gwajin asibiti da aka gabatar a kotu.
Bayan haka da yake bayanin a kotun dalibin ya ce malamin sa Emelogu ya fara lalata da shi bayan da ya fara koyar da shi idan aka tashi makaranta, wato ‘Lesin’
“Kulum idan yana koya min karatu sai ya ce mu shiga ban daki a nan ne mu ke yin abin, ya ian tsorata ni cewa idan ban yi ba zai kada ni a jarabawa.
“Da na gaji shine na yi fito fili na fada sai aka kai kara ofishin ‘yan sanda.
Soladoye ya yi kira ga makarantu da su matsa bincike kan ma’aikata da malaman da suke dauka domin koyar da yara.
Ya kuma kara yin kira ga dalibai da su rika daure wa suna kai karar duk wanda ya ci zarafin su a makaranta da wuri.
Discussion about this post