Gwamnatin jihar Anambra ta ce ta ceto wata yarinya ‘yar shekara 19 da ake zargin wasu maza shida sun yi wa fyade a garin Anam da ke karamar hukumar Anambra ta Yamma a jihar.
Kwamishiniyar mata da walwalar jama’a ta jihar Ify Obinabo, ta shaidawa manema labarai a ranar Asabar cewa an kama wadanda ake zargin.
Wadanda ake zargin sun hada da Afam Ezenwa mai shekaru 17 da Chijioke Ifeanyi mai shekaru 20 da Collins Obadom mai shekaru 18 da Abuchi Okechukwu mai shekaru 16 da Chima Obiekezie da Sunday Okafor mai shekaru 27.
Obinabo ya ce an mika shari’ar zuwa sashin binciken manyan laifuka na ‘yan sandan jihar domin ci gaba da bincike.
“An ceto wanda aka yi fyaɗe kuma tare da hadin gwiwar ‘yan sanda, an kama wadanda ake zargin. Ma’aikatar za ta tabbatar da cewa an hukunta su kamar yadda yake a doka.
Kwamishinan ya koka da yadda ake yawan aikata laifuka a tsakanin musamman matasa sannan ya yi kira ga iyaye da su maida hankali matuka akan tarbiyyan iyayen su.
Budurwar da aka yi wa fyaɗe ta bayyana yadda waɗannan matasan suka yi mata fyade bayan rikon su da ta rika yi.
” Ina hanyar zuwa gida ne fa, sai waɗannan matasa suka dira min, suka yi wuf da ni sai ɗakin su. Haka fa suka rika yin lalata da ni ɗaya bayan ɗaya wani daga cikin su na ɗauka da waya.
” Ina ta rokon su amma ina, babu wanda ya saurareni. Da suka fatattake ni na kama ganyar gida sai wasun su suka tare ni suka ce in cire kamfai na in basu, na cire na basu.
Mahaifiyar yar ta ce haka waɗannan matsa suke yi a unguwan. Ba ƴar ta ce ta farko ba, idan suka yi lalata da mace sai su kwace kamfan ta. Bayan ƴan kwanaki sai a ji ta mutu.
Discussion about this post