Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, Taoreed Lagbaja, ya jaddada cewa Sojojin Najeriya sun tsara hanyar magance rikicin jihar Filato.
Lagbaja ya bada wannan tabbacin a ziyarar da Gwamnan jihar Filato, Caleb Muftwang ya yi masa, ranar Litinin, a Abuja.
Ya ce mafi yawan faɗace-faɗace a Filato matsala cewa tsakanin masu noma da masu kiwon a cikin wasu wurare.
Amma kuma ya ce wanda ya faru baya-bayan nan a Mangu, abin damuwa ne sosai ga sojoji da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.
“Tabbatar
maka cewa wannan matsala da ka kawo
inda ya fi dacewa a ɗaukar mata yadda za a iya magance ta.”
“Mun fito da wasu hanyoyi, waɗanda za a iya cewa an magance matsalar.”
Lagbaja ya ce Gwamna ya yi taro da masu ruwa da tsaki, domin a samu zaman lafiya, a bar tashe-tashen hankula.
Ya kuma shawarci Caleb da a fito da tsarin tsaro na cikin gida.
Haka kuma ya shawarci Gwamna ya fito da rahotannin baya, domin ya ga abin da ya dace a yi a baya, amma ba a yi ba.
Discussion about this post