Gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang ya Saka dokar hana walwala na sa’o’I 24 a karamar hukumar Mangu.
A wata takarda dake dauke da sa hannun Gyang Bere, Kakakin gwamnan ya nuna cewa gwamnati ta saka dokar ne bayan rikicin da aka yi a karamar hukumar a kwanakin nan.
Bere ya ce gwamnati ta dauki shawarar haka ne bayan tattauna wa da manyan hafsoshin tsaron jihar.
Ya ce gwamna Mutfwang ya tabbatar cewa gwamnati za ta ci gaba da kokari wajen ganin ta kawo karshen rikicin da ake fama da su a fadin jihar.
Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa maharan sun kai hari kauyen Sabon Gari a karamar hukumar Mangu inda suka kashe mutum 9 sannan suka babbake gidaje 6 a kauyen.
Wani basarake a kauyen Kuma Shugaban kungiyar ‘Global Society for Middle Belt Heritage’ Jerry Datim ya ce maharan sun afka wa kauyen a daren Asabar.
“Zuwa yanzu mun samu gawar mutum 9 sannan an kona gidaje shida.
Discussion about this post