Gwamnan Jigawa Umar Namadi ya kai ziyarar bazata babban asibitin Dutse inda ya kama wasu ma’aikatan lafiya a asibitin na siyar da magunguna da aka tanada domin bai wa yara ‘yan kasa da shekara biyar kyauta.
Kakakin gwamnan Hamisu Gumel ya ce gwamna Namadi ya yi matukar nuna ɓacin ran sa game da abin, yana mai cewa hakan zai gurgunta tsarin bunkasa fannin lafiya da gwamnatin jihar ta saka a gaba.
“Gwamna ya ce kusan duka marasa lafiyan da aka tattauna da su sun bayyana cewa siyar musu da magani a ke yi a asibitin, bayan kuma ashe kyauta ya kamata a rika ba su suna baiwa ƴaƴan su.
” Sannan kuma ya ce gwamnati ba za ta kyale waɗanda suke aikata irin haka ba da kuma duk wanda ke yi wa kokarin gwamnati na gyara fannin lafiyar jihar zagon kasa ba.
Gwamna Namadi ya yi matukar nuna rashin jin ɗaɗin sa game da halin da ya iske asibitin. Babu tagogi, babu gadajen arziki da mayafai, sannan kuma ba akula da asibitin da marasa lafiya yadda ya kamata.
Bayan haka gwamnan ya kai irin wannan ziyarar bazata sakatariyar jihar, inda ya iske ba ƙanana ba har da manyan ma’aikatan gwamnati ba su zo aiki ba.
Cikin manyan sakatarori 22 da ake dasu a jihar, 3 ne kacal ya samu sun zo aiki a lokacin da ya ziyarci sakatariyar.
Discussion about this post