Majalisar Tarayya ta ce Babban Bankin Najeriya, CBN ya gaggauta tsayar da tsarin tilasta wa kwastomomi bayyana wa banki shafin soshiyal midiya da sada zumuntar su.
Majalisa ta ce tsarin ya karya dokar Sashe na 37 a cikin Dokar 1999.
Ɗan Majalisar Tarayya keleche Nwogu da wasu takwas su ka yi tunanin matsalar da ke tattare da sabon tsarin, wanda a cewar su ya tauye haƙƙin masu ajiya a bankuna.
Wannan sabon tsarin sanin shafi na soshiyal midiya ɗin masu ajiya a bankuna, CBN ya ce ya fito da shi saboda da tsaro.
“Banki na da suna, lambobin waya, lambar BVN da sauran bayanan mu. Don haka tsarin bayyana shafuffuka na soshiyal midiya ba shi dace ba”
Ya ce wannan lamari ya shafi ayyukan EFCC da sauran su.
Saboda haka majalisa ta ce a binciki abubuwan haka kuma kwamiti ya tabbata ya lura da gaske cewa an yi aiki da gargaɗin da suka yi.
Discussion about this post