Wasu daga cikin mazauna jihar Kaduna sun bayyana wa wakilin PREMIUM TIMES HAUSA cewa tun ba aje ko’ina ba sun fara kewar tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai.
Tun bayan rantsar da gwamna Uba Sani mutanen Kaduna ke zura Ido su ga ko akwai wani sabon abu da gwamnan zai yi a tashin farko da zai nuna lallai an samu canjin sabon shugaba a jihar, amma kuma ko don saboda sabo ne mutane dai sun ce shiru su ke ji kamar za’ayi ba za ayi ba.
Baban abin da ya fara jirkita tunani da jefa mutanen jihar cikin tunani mai zurfi shine, a karon farko gwamna Uba Sani ya soma ne da nada wasu daga cikin gaggan ‘yan adawan tsohon gwamnan jihar Nasir El-Rufai
Sanin kowa ne cewa tun a zangon farko na gwamnatin Nasir El-Rufai suka saka kafar wando daya da malamin jami’a kuma kasurgumin dan adawa da tsohon gwamnan, John Dan Fulani.
Amma daga hawan sabon gwamna Uba Sani, Danfulani na daga cikin jerin wadanda ya fara nadawa hadiman sa.
Sannan kuma ga tsohon dan majalisa Sama’ila Suleiman, wanda har zuwa ranar zabe, ya rika caccakar gwamnan jihar a wancan lokacin yana masa habaici da cin fuska yadda ya ga dama. Amma kuma Uba Sani shima ya jawo shi ya yi masa nadin hadimin sa.
Mutane da dama na ganin irin kusancin dake tsakanin gwamna Uba Sani da El-Rufai, ya kamata ace irin wannan shawara tare su ka yi shi tun a farko domin guje wa kawo raini a tsakanin sa da wadancan mutane.
Akilu Sani ya ce ” Ni dai ina ganin da ya dan dakata zuwa wani lokaci kafin idan ma zai saka wadannan mutane da ba su ga miciji da tsohon gwamna sai ya nada su. Kowa ya san irin cin fuska, da izgilancin da Sama’ila ya yi wa Nasir El-Rufai, sannan kuma ace wai abokin ka ya zama gwamna, sai a tashin farko ka dawo da su cikin gwamnatin ka, tun kafin ka canja giya.
” Amma dai kowa da irin salon mulkin sa, ko da ace dai suna tare da El-Rufai, ba zai ji dadi ba a ce wai daga hawa mulki ka kira makiyan sa ka saka su cikin gwamnati, idan za ka yi haka sai ka bari sai an dan kwana biyu. Wannan yana nuna maka cewa akwai sauran rina a kaba: Safiyan Isah
Mutane da da dama sun ce, a yanda gwamnatin ta faro, yanzu wata daya cur da ‘yan kwanaki, ba a san inda gwamnatin ta dosa ba tukunna, ba a fara jin ko akwai wasu abubuwa da gwamnatin ta saka a gaba ba wanda sune ake so a fi maida hankali akai. Ko da ko ta hanyar ambatar su ne kamar yadda wasu gwamnonin suka fara yi.
Sai dai akwai yakinin cewa daya ke gwamnan Sani, ana yi masa ikirari da gogarman aiki ne, za a samu ci gaba masu ma’ana nan ba da dadewa ba.
” Muna yi masa fatan alkhairi sannan kuma muna masa fatan nasara. Mutum ne mai kirki da son jama’a. Za mu sa ido mu gani Allah ya ba shi Sa’a” In Ji Bello Malaga, Mazaunin Kaduna.
Discussion about this post