Tsohon gwamnan Edo, Kuma zaɓaɓɓen sanatan Edo, Adams Oshiomhole ya bayyanawa mutanen kananan hukumomin da suka zaɓe shi sanata cewa, kila yanzu da ya ma mutu, da ace ba su zaɓe shi sanata ba.
Oshiomhole ya bayyana haka ne a wurin taron bikin taya sa murna da aka yi a jihar.
” Ina yi muku godiya matuka da wannan karamci da kuka nuna min, amma kuma ina so ku sani da ace ba ku zaɓeni ba da jini na ya tashi kila zuwa 240/360, idan ina ma raye kenan.
” Domin da ƴan adawa sun biyo ni har gida sun rufe ni gida sun yi rugurugu da kasusuwa na saboda tsananin kiyayya da jin daɗin na faɗi zaɓe amma ku ka ce musu ba su isa ba da kuri’un ku.
” Gwamnoni da yawa sun faɗi zaɓen neman kujerar sanata, da ya zama min abin kunya da a ce ni ma na faɗi zaɓen.
Tinubu ya ce wani abu da ya faranta mishi rai shine, yadda jam’iyyar APC, da ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu ya lashe duka mazabun yanki Edo Ta Tsakiya.
” Zan dauki alkaluman zaɓen innje har gaban Tinubu in nuna masa cewa toh ga shi nan. Mutane na ba su ba mu kun yia sun zaɓe mu 100 bisa 100.
Discussion about this post