Gwamnatin tarayya ta yi tanadin sama da naira tiriliyan daya a cikin watanni biyu da suka gabata bayan cire tallafin man fetur, in ji shugaba Bola Tinubu.
A jawabin da ya yi ranar Litinin da daddare, Tinubu ya ce ƴan Najeriya za su ragargaji ɗaɗi nan ba da daɗewa ba saboda gwamnatin sa ta bijiro da ayyukan ci gaba da waɗanda za su kawo wa ƴan Najeriya sauƙi a rayuwa.
Ina sane da wahalar da kuke fuskanta. Ina fata akwai wasu hanyoyin da za abi amma babu. Idan da akwai, da na bi wannan hanya. Buri na shi ne in ga cewa ƴan Najeriya su samu watayawa yadda suke so kamar yadda muka yi musu alƙawari.
Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta fitar da Naira biliyan 200 daga cikin Naira biliyan 500,000 da majalisar dokokin kasar ta amince da su don noma manyan amfanin gona a kasar nan don magance hauhawar farashin kayayyaki.
” Muna kuma sa ido kan illolin da farashin canji da hauhawar farashin man fetur ke haifarwa. Kuma za kawo karshen sa.
” Ina so in tabbatar muku cewa kowa ya kwantar da hankalin sa ya ci gaba da hakuri, muna dab da fita daga wannan tsanani duhu zuwa ga hake mai ɗorewa.
Discussion about this post