In muka yi nazari da bayanai na harsashen da hukumar da ke kula da chanjin Yanayi ta Kasa, wato NiMET da kuma halin da daminar mu take ciki a yanzu. A kwai abubuwan da ya zama wajibi a hankalta a kai, domin kadda a samu karin karaya a kan targade.
Daman a yanzu ma a na fama da tsadar cimaka da karancin sa, sakamakon abubuwa da dama da suka hada da masifar ambaliyar da shafi manoman mu a bara.
A wanna shekara da muke ciki, daminar wannan shekarar tana cike da kalubale, da ya hada da, jinkirin sauka da samun karancin ruwan sama da samun dogon bartaye na saukar ruwan.
A kiyasin adadin ruwan da a ke samu a kowace shekara a Jahar Jigawa yakai 5000mm zuwa 7500mm a kowace shekara.
Amma a harsashen wannan shekarar ruwan saman da zai sauka bai wuce 4500mm zuwa 7400mm.
Harsashen hukumar mai taken 2023 Seasonal Climate Prediction (SCP), wanda yake bayanin chanjin yanayin da za a samu a wannan shekarar, ya nuna cewa, za a samu jinkirin samun ruwan sama, kamar yadda a ke samu a baya, za a samu jinkirin samun ruwa a farkon damina a watan June da July.
In munyi nazari, wannan lokacin shine amfani yake yabanya, karancin samun ruwa, kan iya maida amfani baya, koma ya kone a wuraren da kasar ke da zafi, kamar yankin Jigawa ta Gabas.
Haka zalika, bayanin SCP din ya nuna yiwuwar samun kamfin ruwan a tsakiyar daminar. In an yi lissafin gibi da bartaye da za a iya samu, to tabbas a kwai iyuwar samun tasgaron girbi a wannan kaka.
Shin menene shirin mu?
Ya kamata Gwamnati Jahar Jigawa ta yi duba da wannan bayanai domin samawa manoma dama al’ummar jahar, sahihiyar hanya da za taimakawa manoman mu da kuma daminar mu.
Bisa da la’akari da tsadar cimaka da karancin abinci da a ke fama da ita a wannan kasar, ya zama dole mu ankare da yanayin da a ke ciki.
alhajilallah@gmail.com
Discussion about this post