Gwamnan Kaduna Uba Sani ya bayyana cewa tun farkon fari bai amince da wai a kirkiro da shirin aika wa mutane kuɗi asusun ajiyar su da sunan tallafi ba.
Ya ce maganar wai a rika tura wa talakawa naira 8,000 duk wata har na tsawon watanni 6, ba abin da ya dace bane a yi.
Idan ba a manta ba, gwamnatin Bola Tinubu ta kirkiro wani shiri na a rika baiwa talakawa naira 8,000 duk wata har na tsawon watanni shida.
Daga bayan suka da shirin ya sha, gwamnati ta dakatar da shi.
” Su waye za a tura wa kuɗin? Wannan shine abin tambaya na farko, sannan waɗanda ya kamata su amfana da shirin ba su da ma ko asusun ajiya na banki, to wa za a tura ma.
” Wani ne kawai zai zauna a birni yana cika aljihun ss da kuɗi da suna wai ana aika wa talakawa tallafi.
Gwamna Sani ya ci gaba da cewa ko a jihar sa ta Kaduna, akwai waɗanda ba su ma cikin kundin rajistan sunayen ƴan kasa don ba a iya kaiwa gare su ba saboda rashin tsaro da aka yi fama da shi a yankunan.
” Yanzu misali karamar hukumar Birnin Gwari, Giwa, Zangon Kataf da wasu wuraren, tsananin rashin tsaro a baya ya sa ba a iya zuwa aikin daukan sunayen mutanen yakin ba da sanin adadin su ba. Yaya za a san wa za ayi wa wani abu na tallafi.
” Gaskiyar magana ita ce akalla kashi 70-75 cikin 100 na mutanen yankin Arewa Maso Yamma ba su da ko da asusun ajiya ne na banki, ta yaya za a aika musu da kudin tallafi.
Gwamnan ya ce dakatar da wannan tsari shine ya fi zama alkhairi idan ainihin talakawa ake so a taimakawa.kuma a yi musu aiki.
Bayan haka ya ce tuni a jihar Kaduna, gwamnati ta fara sabonta rajistan ta domin mutanen da ba su samu shiga a baya ba a saka su ciki a san da su.
Sannan kuma ya karyata raderadin da ake yadawa wai an ba su biliyoyin kuɗi domin talakawan jihohin su.
” Tun da aka rantsar da ni gwamnan Kaduna, babu sisi da aka bani, saboda haka madi cewa wai ana raba kudi, su su ka san inda suka ji wannan magana.
Gwamna Sani ya yi waɗannan bayanai ne a hira da yayi da talabijin ɗin Arise ranar Juma’a.
Discussion about this post