Asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya UNICEF ya bayyana cewa Najeriya na bukatar a rika gina dakunan bahaya akalla miliyan 3.9 duk shekara domin cin ma burin hana yin bahaya a waje daga nan zuwa 2025.
Shugaban shirin WASH Jane Bevan ta sanar da haka a taron masu kasuwancin dakunan bahaya a kasar nan da aka yi a Abuja ranar Litini.
Bevan ta ce zuwa yanzu dakunan bahaya 180,000 zuwa 200,000 ne Najeriya ke ginawa duk shekara amma kuma ba su isa ba.
“Duk shekara Najeriya na asarar naira biliyan 455 saboda rashin tsaftace muhalli.
Babban sakatariyar ma’aikatar ruwa ta gwamnatin tarayya Didi Waldon-Jack ta tabbatar cewa kungiyoyi masu zaman kansu na da rawar da za su taka domin nasarar wannan aiki da aka saka a gaba.
Tace gwamnati za ta hannu da su domin a samu nasa akai.
Discussion about this post