Shugaban ECOWAS, kuma shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya gargaɗi masu son kawo ruɗani da cikas ga gwamnatin Kasar Nijar da su shiga taitayin su.
A wata sanarwa ranar Laraba wacce ta fito daga ofishin sa, Tinubu ya ce shi da sauran mambobin Kungiyar ECOWAS na lura da abinda ke faruwa a kasar ka-inda-na-in.
” Wannan gargaɗi ga waɗanda suke kokarin kawo cikas ga zaɓaɓɓiyar gwamnati mai ci a kasar Nijar. Kada wani ko wasu su kuskura su kawo ruɗani a wannan ƙasa.
” Mu saka ido kuma muna bibiyar abinda ke faruwa a kasar. Ba za mu bari a kawo wa dimokraɗiyya cikas ba, wacce ita ce jama’ar kasar suka amince da suka zaɓi shugaban su. Ba za mu bari wani ya kawo wa tsarin dimokuraɗiyya matsala ba.
Tinubu ya ce a matsayin sa na shugaban ECOWAS, ba zai yi kasa a guiwa ba wajen ganin ba a kawa tangarɗa ga gwamnatin dimokraɗiyya a Nijar.
” Da ni da sauran shugabannin kasashen ECOWAS duk muna sauraren abinda ke gudana a kasar kuma ba za mu daga wa koma wanene kafa ba, muddun zai kawo cikas ga dimokraɗiyya da ake mora a Jamhuriyyar Nijar.
Shugana Tinubu, a jawabin sa lokacin da aka zaɓe shi shugaban ECOWAS a farkon wannan wata, ya gargaɗi sojoji masu ra’ayin amfani da karfin soja su kawo tangarɗa ga gwamnati a kasashen yankin da su shiga taitayin su. Cewa ECOWAS ba zata bari a rika kawo wa gwamnatocin da aka nada su ta haryar Dimokraɗiyya cikar ba kuma a zuba musu ido.
Discussion about this post