Hukumar Alhazai ta Kasa ta karyata raɗe raɗin da ake yaɗawa wai citar Kwalera ce ta barke a masaukin Alhazan Kano a Makka, wai har an kwantar da mutum tara a asibiti.
Shugaban sashen kula da marasa lafiya na hukumar, Hassan Galadima ya yinƙarin bayani akan haka.
Galadima ya ce ba Kwalera ba ce Alhazan suka yi fama da shi, yamutsewar ciki ne kawai bayan sun ciwo garaugarau ɗin su a wuraren da aka ja musu kunne kada su rika zuwa cin abinci a can.
” Tumbin Alhazan da aka kwantar ya yamutse ne bayan sun yo ciye-ciye a wuraren siyar da abinci da aka yi musu gargadin kada su rika siyan abinci a wuraren, wato garaugarau.
” Su tara ne suka barke da gudawa, bayan sun ciwo garaugarau din su a inda aka hana Alhazai zuwa siyan abinci su ci. Dukkan su an duba su kuma tuni sun warke sarai.
Galadima ya kara da cewa babu wani da ya kamu da irin haka, domin ba Kwalera ba ce su ka yi fama da.
Discussion about this post