Rahotanni na nuna cewa Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu ya yi murabus da shugabancin jam’iyyar.
Daily Trust ta ruwaito cewa Adamu ya mika takardar murabus daga shugabancin APC ranar Lahadi, sai dai da aka nemi ji ta bakin sa ya bayyana cewa ba zai yi magana game da murabus da yayi daga kujerar shugabancin APC ba sai shugaban kasa Bila Tinubu ya dawo daga Kenya.
” Ba zan faɗi abinda ake cika ba tukunna sai shugaban kasa Bola Tinubu ya dawo daga taron da ya ke halarta a ƙasar Kenya.
Sai dai Daily Trust ta buga cewa Adamu ya mika takaradar sa ga shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ranar Lahadi.
Discussion about this post