An maka tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Ogun na PDP a gaban kotu, a kan zargin raba ATM 200,000 da kuma sayen ƙuri’u na naira bilyan 2 a ranar zaɓe.
An gurfanar da Ladi Adebutu a Babbar Kotun Abeokuta, tare da wasu mutum tara da ake zargin taya shi shirya gada-gada a ranar zaɓe.
Amma kuma Adebutu bai halarci Kotun ba, saboda ya fice daga kasar bayan zaɓen 18 Ga Maris.
Idan ba a manta ba ‘Yan sanda sun ce Adebutu wanda ya yi takarar gwamnan Ogun a ƙarƙashin PDP, ya yi watandar naira biliyan 2 a faɗin jihar, domin a sayi ƙiri’un masu zaɓe a zaɓen gwamna na ranar 18 Ga Maris.
Wannan zargin da ake yi masa, ya na cikin rahoton da ‘yan sandan bincike su ka gabatar wa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda.
Shugaban APC na Jihar Ogun, Abdullahi Sanusi ne ya aika wa Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ogun takardar ƙorafi, su kuma su ka gudanar da bincike.
Yadda Adebutu Ya Shiga Tsomomuwa:
Abdullahi Sanusi ya rubuta wasiƙar ƙorafin ce zuga ga ‘yan sanda, a ranar 18 Ga Maris, wato ranar zaɓe. Ya yi adireshin wasiƙar ga Sufeto Janar na Ƙasa.
A cikin takardar ƙoƙarin, ya ce Adebutu ya riƙa raba katin ATM wanda kowane an loda masa Naira 10,000 a cikin asusun. An riƙa raba su a ranar zaɓe.
Daga nan aka naɗa ‘yan sandan bincike a ƙarƙashin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda, Mohammed Babakura, da ke Ofishin Binciken Manyan Laifuka (CID), a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Adebutu ya samu ƙuri’u 262,383, ya zo na biyu, shi kuma Gwamna Dapo Abiodun na APC, ya sake lashe zaɓe a karo na biyu kenan, da ƙuri’u 276,298.
Rashin nasarar da Adebutu ya yi da bambancin ƙuri’u 14,000 kacal, sai ya garzaya kotun sauraren ƙararrakin zaɓe, ya maka Gwamna Abiodun ƙara a kotu.
Discussion about this post