Kwararrun jami’an lafiya sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta ci gaba da wayar da kan mutane game da hanyoyin kare jarirai daga kamuwa da cututtuka a lokacin da suke cikin uwayen su domin dakile yaduwar cutar Hanjamau, Hepatitis da cutar sanyi ‘Syphilis’.
Kwararrun sun fadi haka ne zama domin inganta lafiyar mata da yara kanana da aka yi a Abuja.
Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasar Amurka CDC ta shirya taron mai taken ‘Kare Jarirai daga kamuwa da cututtukan kanjamau, Hepatitis B da cutar sanyi ‘Syphilis’.
Kodinatan shirin dakile yaduwar cutar kanjamau da cutar sanyi ta kasa NASCP Bashorun Adebobola ya ce babban burin shirin shine kare yara daga kamuwa da cututtuka.
Adebobola ya ce gwamnatin Najeriya ta yi kokarin ganin ta kare yara daga kamuwa da cututtuka amma ya ce har yanzu akwai sauran aiki a gaba.
Ya ce kamata ya yi gwamnati ta mai da hankali wajen ganin mata masu ciki na zuwa asibiti domin yin awon ciki.
Sakamakon binciken da NDHS ta gudanar a Najeriya a shekarar 2018 ya nuna kashi 67% na mata masu ciki ne ke zuwa awon ciki a asibiti.
Sannan a shekarar 2022 an gano cewa yara kashi 34% ne ake yi warigakafin cututtukan.
Discussion about this post