Shugaban hukumar Raya Babban Birnin Tarayya FCDA Shehu Ahmed ya bayyana cewa za ta rusa duk gidajen da aka gina su akan hanyar ruwa a Abuja.
Ahmed ya sanar da haka ne a wata takarda da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Ya ce rusa gidaje irin haka ya zama dole saboda su toshe hanyoyin ruwa da hakan ke assasa ambaliya idan aka yi ruwa mai yawa.
“Gidajen da ke Trademark na daga cikin gidajen da muka yi wa shaida domin rusa su sannan tun a shekarun da suka gabata muke sanar da mazaunan wurin halin da ake ciki amma duk sun yi watsi da maganar mu.
“Mun sanar wa mazauna rukunin gidajen Trademark da su yi gaggawar tashi a wannan wuri saboda duk shekara sai an yi irin wannan ambaliyar amma suka yi mana kunnen uwar shegu.
“FCDA za ta rusa ofishin ‘yan sandan dake Trademark amma kuma ta ware wuri wa jami’an tsaron domin ci gaba da aikinsu na samar da tsaro.
Ya ce tun farko an gina rukunin gidajen Trademark ba tare da amincewa FCDA ba. Hakan ya sa wurin ke yawan fama da matsalar ambaliya.
“Wuraren da dama hanyar ruwa ne bai kamata a yi gini a wurin ba amma mutane ba su ji ba.
Discussion about this post