An nada ‘ya’yan tsoffin gwamnonin da ke majalisar wakilai a matsayin shugabannin manyan kwamitocin majalisar.
Bello el-Rufai, dan Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna; Olumide Osoba, dan Segun Osoba, tsohon gwamnan jihar Ogun da Suenu Ibori diyar James Ibori, tsohon gwamnan jihar Delta na daga cikin shugabannin kwamitoci 134 da kakakin majalisar Tajudeen Abbas ya sanar a ranar Alhamis.
Sauran sun hada da Adegboyega Adefarati, dan Adebayo Adefarati, tsohon gwamnan jihar Ondo da Olamju Akala, dan Alao Akala, tsohon gwamnan jihar Oyo.
An nada Bello El-Rufai, shugaban kwamitin hankokin Bankuna na majalisar. Abbas ya nada diyar Ibori a matsayin sabuwar shugabar kwamitin hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC).
Adefarati, wanda ke wakiltar mazabar Akoko ta Kudu-maso-Gabas/Kudu-Yamma, shi ne shugaban kwamitin majalisar kan harkokin kwadago, samar da ayyukan yi.
Olumide Osoba shi ne shugaban kwamitin shari’a na majalisar.
Olamju Akala, ne shugaban kwamitin matasa na majalisar wakilai. Yana wakiltar mazabar tarayya ta Ogbomosho ta jihar Oyo.
Discussion about this post