Kasancewa ta a cikin sha’anin siyasa tare da bibiyar yadda alkaluma suke kai-wa-da-komowa ya bani damar fahimtar wani wawakeken gibi da yan siyasar mu suka kirkirar mana a cikin zukatanmu, kuma wannan shi ne babbar silar koma bayan alumma ta fuskoki daban-daban na rayuwa.
Wannan wawakeken gibin da shuwagabannimu suke bijiro mana dashi domin samun cikakken iko akan tunaninmu shi ne, sun darsa mana tsana da kiyayyar dukkanin abin alheri ko cigaba indai ba daga bangaren jam’iyyar mu ko dan siyasar mu yake ba. Haka zalika shima daya bangaren yana yiwa kowane aikin alheri ko na cigaba da abokanen hamayyar su zasu kawo ko dabbaga domin cigaban jiha ko kasar mu.
Wannan shi ne irin yanayin da kaso mafi rinjaye na yan siyasa suke ciki, kalilan ne daga cikin alummar gari suke iya tsayawa akan tunanin me zai kawowa alumma cigaba da saukin rayuwa sabanin wancan rukunin mutanen da suke fifita ra’ayin siyasa ko jam’iyya akan cigaban alumma da rayuwar su. Akwai bukatar mu tashi tsaye wajen fadakar da alumma muhimmanci fifita abin da yake da alfanu da kuma abin da bazai ciyar da alumma gaba ba.
Ba wai ina nufin cewa rike ra’ayin siyasa kuskure bane, babban kuskure ace mutum bashi da ra’ayin kashin kansa domin duk wanda bashi da ra’ayi bai kammala ba a rayuwa. Amma akwai bukatar hankali da tunani su rinjayi ra’ayoyinmu na siyasa ta yarda zamu iya tantance fari da baki ba tare da bawa son rai ko fifita bukatun siyasa akan cigaban alumma da rayuwar mu ba.
Rattabawa
Umar Aliyu Musa
oumaraliyu@gmail.com
Discussion about this post