Gwamnan Kano, Abba Yusuf ya ce a daina yi wa rushe-rushen da ya ke yi fadin jihar mummunar fassara.
Tun bayan rantsar da Abba Yusuf gwamnan Kano ya fara rusau na wasu gine-ginen da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ya raba ba tare da an bi ka’ida ba.
Da ya ke jawabi a lokaci da sarakunan Gaya da Kano, Aliyu AbdulKadir da Aminu Ado Bauero suka ziyarce shi a gidan gwamnati, gwamna Yusuf ya bayyana wa sarakunan cewa baya nadamar abinda ya ke yi a fadin jihar, musamman na rushe-rushe da gwamnatin sa ke yi.
” Muna yin abin da ya dace ne domin talakawa. Kuma ina tabbatar muku cewa ƴan adawa ne ke ruruta abin amma, abinda nake so kowa ya sani kuma ‘a rubuta ya ajiye shine’ abinda za mu yi kafin karshen wa’adin mulkin mu, za ayi matukar yabawa.
Discussion about this post