Wata ɗaya bayan cire tallafin fetur har da da yawan jama’a sun yi gigicewar afkawa cikin tsadar rayuwar da ba a taɓa ganin kamar ta a shekaru masu yawa a baya ba.
Yayin da farashin kayan abinci ya cillawa sama da kashi 28% a shekarar da ta gabata, a wasu yankunan farashin kayan abinci kamar doya, shinkafa, wake, gero, masara da shi dawa na nema su gagari talakawa.
Gidaje da dama sun koma dafa abinci sau 2 da safe da rana. Yawancin yara da ba su saba da garɗin gero ba sai shayi, yanzu dai su ma sun fahimci ashe shayi ruwa ne, sun koma a shan
kunu.
Cimakar mutanen karkara kamar gwaza, dankali, zogale da sauran su ne ake gwagwagwar saye a kullum.
Yayin da motocin haya suka ragu, haka masu safarar da ba wadataccen samu sun rage yawan fita.
Yara da ɗalibai da ake kaiwa makaranta a mota, da yawa a halin yanzu a Keke NAPEP ake kai su makaranta.
Da dama sun daina amfani da janareto saboda rashin wuta. Wasu sayar da shi suka yi, suka sayi abinci, wasu kuwa sola suka koma.
Da yawa rabon su da ana tun ranar Sallah Babba, saboda rayuwa ta yi tsada.
Masu faram-faram da bako, su na gudun kada a kai masu ziyara a wannan lokaci.
Matalauta sai kara yawa su ke, kamar yadda mabarata ke kara yawa su na gararamba a cikin gari da tashoshin mota.
Marasa galihu da dama sun koma bara da kuma riƙon tallafin kuɗaɗe a masallaci.
A gidajen masu bada sadaka, dandazon mabarata da ‘yan maula sukan shafe tsawon lokaci kafin a fara raba masu kuɗaɗen da za su iya samun abin sawa a bakin salati.
Discussion about this post