Daga ba makanike gyaran mota, sai ya waske da ita, wata ɗaya cur ba a ganshi ba, an kama shi a Taraba
Ƴan sandan Nasarawa sun kama wani makanike mai suna, Sani Musa, wanda daga ba shi mota ya gyara sai ya waske da motar, ya kama gaban sa.
An yi wata ɗaya cur ana neman sa ba a ganshi ba.
Daga nan ne fa ƴan sanda suka fantsama farautar sa har ya kai ga an kama shi a Gembu, jihar Taraba.
Bayan an gudanar da bincike sai aka gano cewa Makaniken, Sani Musa ya har ya gama cinikin motar zai siyar naira miliyan 2.5.
Discussion about this post