Sakamakon zaɓen shugaban kasa na Saliyo da aka bayyana a yau Talata ya nuna shugaban kasar Julius Bio ya murkushe babban abokin takarar sa na jam’iyyar APC, Samura Kamara.
Sakamakon zaɓen da aka bayyana ranar Talata ya nuna cewa Bio ya samu kashi 57 cikin 100, da hakan ya sa ya kada abokin hamayyar sa Kamara na APC da ke da 41 cikin 100 na kuri’un da aka jefa.
Shugaban, mai shekaru 59, ya sake tsayawa takara ne bayan wa’adin farko na shekaru biyar da ya kammala wanda aka yi fama da hauhawar farashin kayayyakin abinci da na masarufi, tsadar rayuwa da kuma tsananin talauci.
A bisa dokar zaben kasar Saliyo, domin samun nasara a zagayen zaben farko, dan takara na bukatar sama da kashi 55 cikin 100 na kuri’un da aka kada, Bio ya samu kashi 56 cikin 100.
Discussion about this post